Darussan Rayuwa | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→HikayaDarussan Rayuwa

Post by , 10 months ago

Category: →Hikaya, 222 Views

Abin da ke tafe wasu ‘yan gajerun hikayoyi ne kyawawa, wadanda karanta kowane guda daga cikinsu ba ya bukatar lokaci mai yawa, to amma fahimta da kuma aiki da su na iya yin tasiri mai girman gaske cikin rayuwarmu da kuma sauya ta.

1. Sakamakon farin da mutanen wani kauye suka fuskanta, sai suka yanke shawarar fita wajen garin don rokon ruwa. A ranar da suka fito wajen rokon ruwa, babu wani daga cikinsu da ya dau lema in ban da wani dan karamin yaro guda…

Wannan shi ake kira IMANI…

2. Daya daga cikin hanyoyin da muke bi wajen wasa da kuma faranta ran ‘ya’ya da kannenmu jarirai, ita ce wurga su sama muna cabewa; shi kuwa wannan jaririn yana ta sheka dariya da farin ciki. Saboda ya san za mu cabe shi ba za mu bari ya fado ba.

Wannan shi ake kira YARDA…

3. A kowane dare mu kan kwanta barci, duk kuwa da cewa ba mu da yakinin za mu farka a raye, to amma duk dare mu kan yi ‘saitin’ agogonmu don ya tashe mu saboda wani aiki da muke son yi.

Wannan shi ake kira (kyakkyawan) fata…

Ta hanyar “imani, yarda da kuma (kyakkyawan) fata’ ga Allah ne za mu iya gina wa kanmu rayuwa mai kyau. A saboda haka mu yi kokari wajen karfafa wadannan abubuwa guda uku.

Allah Ya Mana Jagoranci

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Related Posts

Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share