Angudanar da Jana’izar Shahidai Biyu Da Jami’an Tsaron Suka Kashe Shekaran a Abuja. | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→LabaraiAngudanar da Jana’izar Shahidai Biyu Da Jami’an Tsaron Suka Kashe Shekaran a Abuja.

Post by , 9 months ago

Category: →Labarai, 194 Views

Angudanar Sallar Jana’izar Shahidai biyu a Suleja, wadan da jami’an tsaron shugaban kasa Muhammadu Buhari suka harbe su a Abuja. Sheikh Abdulhamid Bello Zariya ne ya jagoranci Sallar.

Jami’an tsaron sun harbe almajiran na Sheikh Zakzaky ne a ranar Talata 09/07/2019, a lokacin da suke gudanar da jerin gwanon limana na cigaba da kira ga gwamnatin Buhari da ta saki Sheikh Zakzaky da take tsare dashi fiye da shekaru uku.

Tun bayan kama Sheikh Zakzakin ne dai almajiran nasa a kullum sukan fito domin yin kira ga gwamnatin da ta gaggauta sakin Malamin kamar yadda Kotu tayi umurni tun a shekara ta 2016.

A kwanukan baya ma wata Kotu ta yi umurni da da a gaggauta fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa da take cigaba da tabarbarewa, kamar yadda kwararrun likitoci suka tabbatar, amma dai har yanzu abin ya citura.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share