Sabon sakon Muhammadu Ibrahim Akan Lafiyar Mahaifinsa | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→Sayyid Zakzaky (H)Sabon sakon Muhammadu Ibrahim Akan Lafiyar Mahaifinsa

Post by , 9 months ago

Category: →Sayyid Zakzaky (H), 196 Views

A Ranar Asabar,  13 ga watan Yuli 2019, dukkanin ‘iyalanmu wadanda a baya na ce; mahukunta’ sun tattauna da su, sun isa Kaduna domin haduwa da mahaifina da mahaifiyata. Sai dai abin bakin ciki, saboda rashin tuntubar juna, ni da kuma lauya ne kadai aka bari su ka gana da su. Sauran kuwa an tilasta musu barin wajen ne da bakin bindiga.

A karshe an kyale mahaifina ya rike wayar tarho, don haka ya zuwa yanzu muna iya tuntubar juna; ga shi kuma an riga an tsayar da lokacin zaman kotu; an kuma yi alkawulla masu yawa. Wannan shi ne abin da zan iya kira da labarai masu dadi.

Labarai marasa dadi kuwa su ne; cewa mahaifin nawa ya fuskanci bugun zuciya karo na biyu. Duk da cewa dai ba mai girma ba ne, amma ba zan iya kaskantar da wadannan manyan matsaloli guda biyu ta fuskar kiwon lafiya da su ka faru a cikin kankanen lokaci ba.

Na riga na kammala dukkanin shirye-shiryen da su ka kamata domin daukar matakin gaggawa a likitance, na kuma tsara duk abin da ya dace. Amma har yanzu muna sauraron “mahukunta” su cika nasu alkawullan na bayar da takardar shiga da fice ( passport) na kasa da kasa, musamman saboda ganin mun ba su dukkanin takardun da ake bukata domin shirya takardar ta shiga da fice cikin sa’oi kadan a ranar Litinin.

Gabanin in kai ga buda baki in ce; Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, gabanin in ce; Allah ya karbi abinshi, ina sake yin kira ga mahukunta da kada su yi kasa a gwiwa; domin kananan abubuwan da ba su kai haka ba, sun kashe mazajen da su ka fi mahaifina karfi, Nufin Allah ne kadai yake ci gaba da kare shi tsawon wannan lokaci.

Ruwan harsasai a jikinsa,buguwa, azabtarwa ta gangar jiki, da cutarwa ta tunani, da wasu abubuwan masu firgitarwa wadanda zan jinkirta ambatonsu zuwa gaba, sun faru a baya. Mahaifina yana da bukatuwa da a kwantar da shi a asibiti, kuma cikin gaggawa.

Zuwa gobe, zan sake yin bayani akan inda mu ka kwana.

Mohammed Ibraheem Zakzaky

13 July 2019

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share