MAYAR MASALLACIN ƘUDUS WAJEN BAUTAR YAHUDANCI BAYAN FITOWAR DUJJAL | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

HomeUncategorizedMAYAR MASALLACIN ƘUDUS WAJEN BAUTAR YAHUDANCI BAYAN FITOWAR DUJJAL

Post by , 9 months ago

Category: Uncategorized, 350 Views

Labarai na ta yin karakaina cewa Yahudawan sahayoniya suna da nufin rusa masallacin Ƙudus domin su gina wajen bautar Yahudanci a makwafinsa. Tambayarmu anan shine yaushe ne ake sa ran faruwan haka ko suke danshirin yin haka?

Amsarmu tana a cikin Alƙur’ani mai girma, sai kuma Attaura da Linjila. Da wasu masadir da suka baiyana hakan da yiwuwar zai iya kasancewa ne a shekarar 2019 miladiyya. Zamu iya riskar wannan amsar a cikin surar Baƙarah aya ta 114. Sai kuma a Revelation babi na 11 na cikin littafin Sabon alƙawari.

Bari mu fara da kawa labarin da yazo daga Injila dangane da Haikalin na Yahudawa.

Shaidu Biyu

1 Sa’an nan aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce mini, “Tashi ka auna Haikalin Allah, da mayanka, da kuma masu sujada a ciki,
2 amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al’ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba’in da biyu.
3 Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi hasashe har kwana dubu da metan da sittin, (1260) suna a saye da tsummoki.”

Wannan abinda ya ya gabata an nuna cewa Yahudu zasu yaye saman Masallacin Ƙudus domin su mayar dashi wajen bautarsu kafin cikar kwanaki 1260 na lokacin yin Ma’arikatus Sa’ah (Harmajidon). Domin ana sa ran faruwar yaƙin ƴanta masallacin Ƙudus zai kasance daga 2022/1444 Allah ne masani.

Lissafin zai kasance a koyaushe daga watan Fabarairu na shekarar 2019. Wannan rusawar da Yahudu zasuyi ga Masallacin Ƙudus zai kasance ne bayan dawowar Annabi Isa(A) a karo na biyu. kamar yanda aka nuna a wasu zantukan nassosin. Domin Yudawa sun kasance masu tsananin gaba da Annabi Isa(A) ba zasuyi imani da shi ba a dawowar tasa. Watau a lokacin da shaiɗanin da suke riyawar zai tseratar dasu zai baiyana, kafin yaƙin Sa’ah da watanni 42, a wannan tsakanin. Kamar yanda aka ambata masu a cikin littafin Malakhi a babi na 4. Suna riya cewa wannan mai ceton nasu na ƙarshen zamani wai shine Annabi Iliyasu(A)

5 “Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai barazana ta Ubangiji ta zo.
6 Zai sāke kawo iyaye da ‘ya’ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”

Ba ina nufin na yarda da cewarsu bane wai wannan Dujjal ɗin da suke sa ran zai cece su a ƙarashen zamani shine Annabin Allah Iliyasu(A). Wanda a Bible ɗin an faɗi sunan ne da cewa Iliya, ba Iliyas ba. Kawai na kawo ne domin shaidar masu abin da yake sunyi imani dashi.

Domin a fahimta ta kamar sunyi taharifin kalmar da take a wurin ne. In muka yi la’akari ta hanyar Hisabi zamuga cewa kalmar sunan Iliya ta yanda ake rubuta sunan da ibraniyanci zamuga cewa adadinsa shine 53. Wannan adadin 53 kuma shine adadin sunan Ahmad, watau sunan Annabi Muhammad(S) da Annabi Isa (A) ya ambata masu a cikin albishir ɗin da yayi ga mabiyansa dangane da Annabi Muhammad (S).

Yazo a cikin Littafin Daniyel littafin da yake bayar da labaran abubuwanda zasu faru a ƙarshen zamani. An ambata a cikin babi na biyu cewa:

28 Amma akwai Allah maɗaukaki mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanakin ƙarshen zamani……… Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa’ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.

Abubuwanda muke gani na tasarrufin Internet yayewar asirrai ne a wannan zamanin, kafin kammalawarsa a ranar Ubangiji (Daular Imam Mahdi(A). Watau abubuwa da yawa na yayewar waɗannan sirrukan zasuyi ta baiyana a tsakanin shekaru bakwai kafin rusa Isra’ila. Waɗannan shekarun bakwai zasu zama masu kuncin gaske. Kamar yanda labarin ya zo a cikin littafin Matta babi na ashirin da huɗu a inda ake bayar da labarin farkon wahala da wahala matsanaciya da ɗan adam bai taɓa ganin irinta ba tun farkon duniya. A lokacin da halin da mutane zai kasance a Falasɗinu yayin da aka rusa masallain Ƙudus.

Dangane da Kiristoci kuwa su sunyi imani da zuwan Yesu Almasihu A zangon ƙarshe na shekaru bakwai kafin zuwan ranar Ubangiji na lokacin yaƙin Armagiddon(Harmajidon). Daza ayi shi a ƙasar Palasɗinu, kamar yanda labarin yazo a cikin Iittafin Sabon Alƙawari Mu ɗauki misali da Injila Dangane da rusa masallacin Ƙudus.

Yaushe ne zamuga rusa mummunan aikin nan da Annabi Daniyel ya faɗa, da zai kasance a inda masallacin Ƙudus yake. Domin mai karatu ya gane domin in lokacin yayi waɗanda suke a ƙasar Yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu

An baiwa Yahudwa da wasunsu labarin ficewa daga ƙasar Palasɗinu a lokacin da suka ga an rusa masallacin Ƙudus an mayar da wurin bautar Yahudanci a makwafinsa. An umarce su da su gudu domin su tsira daga yaƙi a ƙarshen zamani.

Amma sai gashi suna iya iyawarsu da dukkan ƙarfin su wajen korar Larbawa Palasɗinawa daga ƙasarsu tun 1948, domin kawai su tattara Yahudawan duniya a cikin Isra’ila. Saboda jiran fitowar Dujjal ɗinsu a shekarar 2019, in sun rusa masallacin Ƙudus sun gina wajen bautar Yahudanci a madadinsa. Sun saɓa da Umarnin da aka basu a cikin Attaura da Injila.

Idan muka koma ga Alƙur’ani kuwa dangane da wannan lamarin, zamu ga labarin rubuce a cikin aya ta 114 na cikin surar Baƙarah.

113- Yahudawa suka ce Kiristoci ba abakin komai suke ba, Suma Kirstoci suka ce Yahudu ba abakin komai suke ba, alhali dukkansu suna karanta littafi. Haka nan waɗanda basu sani ba suke faɗin irin zantukansu, Allah zaiyi hukunci a tsakaninsu ranar Tsayuwar Imam Mahdi, a cikin abin da suka kasance suna saɓawa a cikinsa.

114- Wanene yafi girman zalunci daga wanda ya hana a ambaci Allah a wuraren yiwa Allah sujada, Yayi hanƙoron rusa wurin sujadar. Waɗannan bai kamata su shiga cikin ta ba sai a cikin halin tsoro, Zasu ƙasƙanta a duniya a ƙarshe kuma su samu azaba mai girma

Waɗannan ayoyin suna yi mana nuni da saɓanin da za asamu a tsakanin Kiristoci da Yahudawa bayan zuwan Annabi Isa (A). Ga kuma taharifin wasu abubuwan masu faruwa da sukayi a cikin Attaura da Injila. Domin Kiristoci sunyi imani da dawowar Annabi Isa (A) a ƙarshen shekaru bakwai. Sukuma Yahudawa sunyi imani da samun wani mai cetonsu a tsakiyar waɗannan shekarun bakwai. Wannan a fahimta ta yana daga cikin abun da zai kawo masu saɓani, kamar yanda ayar ta nuna.

Ayar ta 114 tayi nuni da hanawar da Yahudawa zasuyi ga yin ibada a cikin masallacin Ƙudus, da sauran masallatai da suka ƙirƙiro su. Suka kuma himmatu wajen ganin sun rusa masallacin na Ƙudus. Dukkan Yahudu zasu koma cikin Isra’ila ne a tsorace domin ta’addancinsu sannan komawarsu ƙasar Palasɗinu nayin nuni ne da cewa, lokacin da za a kawo ƙarshen su ya kusa kasancewa. Ayar tana nuni ne da komawar su Yahudawan cikin ƙasar Palasɗinu bayan rusa masallacin Ƙudus.. Dalili kuwa a ayar an fara ambaton ( Suka himmatu domin rusa masallacin ) sannan aka ce daga baya ( Su waɗan nan (Yahudawan) bazasu shigeta ba(Ƙasar Palasɗinu) sai a tsorace ). Watau bayan sun rusa masallacin sun gina wajen bautarsu na Yahudanci.

Shekarar 2019 da muke hasashen a cikinta ne za su rusa masallacin na Ƙudus da muka ce an ambaci labarin a aya ta 114 na cikin surar Baƙarah. Dalili shine; da zamu duƙufa da lissafa kalmomin ayoyin surar Baƙarah daga farko har zuwa ƙarshen aya ta 114 zamuga cewa kalmomi ne guda 2019. Da muke ganin adadin yana yin nuni ne da shekarar 2019.

Har yanzu da zamu lissafa ayoyin daga aya ta 114 na cikin surar Baƙarah zuwa ayar ƙarshe na surar Isra’i, surar da take bayar da labarin kawo ƙarshen ɓarnar Yahudawa a karo na biyu. Anan ma zamuga cewa ayoyi ne guda 2019.

Allah ne mafi sani.

Allah ka taimaki bawanka da ake zalunta mai son kawo gyara a ƙasarmu Nijeriya ka yalwata lafiyar sa albarkacin shugaban zamaninmu amincin Allah su tabbata a gare shi. Wanda zai kafa tutar adalci a dukkan faɗin duniya.

Muhammad Sani Ra’is, Funtua.
+2347034595991
28101440
01072019

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share