Hakkin Jama’ar Kasa A Kan Mai Mulki | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→TunatarwaHakkin Jama’ar Kasa A Kan Mai Mulki

Post by , 8 months ago

Category: →Tunatarwa, 199 Views

Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: “Amma hakkin jama’ar kasa da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama’arka ce saboda rauninsu da kuma karfinka, don haka wajibi ne ka yi adalci a cikinsu, ka zama garesu tamkar uba mai tausayi ne, ka yafe musu jahilcinsu, kada ka gaggauta musu da ukuba, kuma ka gode wa Allah a kan abin da ya ba ka na karfi a kansu”.

Adalci tsakanin al’umma ba tare da fifiko ba shi ne kashin bayan samun nasarar shugaba, wannan adalcin yana da ma’ana mai fadi don ya hada da adalci a siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa, da addini, da al’adu, da rayuwa, da tunani, da dukkan wani abu da yake kewaye da al’umma na hakkin jiki, ko ba najiki ba.
Al’umma tana da hakki a matsayinta na Daidaikun mutane da al’umma a dunkule, wacce take da hakkin jagoranta ya kare mata hakkin kare zahirin rayuwarta, da kuma hakkin kare mata badinin rayuwarta, ya auna kowannensu da ma’auni daya, ya tausasawa da tausayawa, ya kawar da tsoronsu, ya biya bukatunsu, ya karbi gaskiya da nasiha gunsu, idan ya ki to sai su koma gaya masa karya, domin ko an gaya masa gaskiya sai ya yi fushi da su.

Suna da hakkin ya kula da lafiyarsu, da tsaftar gari , da kula da tsarin birane da gidaje wadatattu, da kula da iliminsu, da kula da tsaronsu, da abubuwan more rayuwa, da kula da annashuwa da wasanninsu.

Imam Ali (A.s) ya ce da Ziyad dan Babansa, a lokacin da ya maye shi da Abdullahi dan Abbas a yankin Farisa da ayyukanta, a cikin wata magana mai tsayi tsakaninsu da ya hana shi game da dada haraji-: “Ka aiwatar da adalci, ka guji tsanantawa (ba tare da hakki ba), da yin zalunci, domin tsanantawa tana jawo kaurace wa wuri, zalunci kuwa yana kawo yaki ne” .
Imam Ali dan Abi Dalib (a.s) yana rubatawa zuwa ga Muhammad dan Abubakar yayin da ya sanya shi gwamnan Misira, yana cewa: “Ka kaskantar da fukafukanka, ka tausasa bangarenka, ka sakar musu da fuska, ka daidaita su a bayar da lokaci da kallo, don kada masu girma su yi kwadayin zaluncinka gare su (talakawa), kuma kada raunana (talakawa da marasa galihu) su yanke kauna daga adalcinsu garesu .
Kuma Allah madaukaki zai tambaye ku zama da bayinsa game da karamin aiki da babba, da na zahiri da na boye, idan kuwa ya yi muku azaba, to ku ne kuka yi zalunci, idan kuwa ya yi afuwa to shi ne ya yi rangwame.
Ku sani ya ku bayin Allah cewa, masu jin tsoron Allah sun tafi da rabon duniya da ladan lahira, sai suka yi tarayya da ma’abota duniya cikin duniyarsu, amma ‘yan duniya ba su yi tarayya da su ba cikin ladan lahirarsu ba, sai suka zauna duniya da mafi kyawun yadda aka zauna ta, suka ci ta da mafi kyawun yadda aka ci ta, sai suka rabauta da duniya kamar yadda masu holewa suka rabauta da ita, suka dauki abin da masu girman kai suka dauka daga gareta, sannna sai suka cirata daga gareta da guzuri isasshe, da kasuwanci mai riba, suka samu dadin gudun haram a duniyarsu, suka samu yakinin cewa su ne makotan Allah gobe a lahirarsu, babu wani nemansu da ake mayarwa, kuma babu wani jin dadinsu da ake ragewa.

Ya ku bayin Allah ku ji tsoron mutuwa da kusantarta, ku yi mata tanadi, domin tana zuwa lamari mai girma, da babbar magana, da alherin da babu sharri tare da shi har abada, da sharrin da babu alheri tare da shi har abada. Wane ne ya fi kowa kusanci da aljanna fiye da mai aiki cikinta! Waye kuma ya fi kowa kusanci da wuta fiye da mai yin aikinta! Ku sani ku abin farautar mutuwa ne, idan kun tsaya mata sai ta kama ku, idan kun guje mata sai ta cimma ku, ta inuwarku lizimtarku (zama tare da ku), ga mutuwa a kulle ta a makwankwadar kanku, duniya kuwa ana nade ta daga bayanku; (wato duk wani minti daya da kuka ba wa baya, sai a nade shi, ba zai sake dawo muku ba!)
Ku ji tsoron wuta da zurfinta mai nisa ne, zafinta mai tsanani ne, azabarta sabuwa ce, gida ne da babu rahama cikinsa, kuma ba a amsa wani kira a cikinta, kuma ba a yaye wani bakin ciki a cikinta.
Idan kuna son tsoronku da Allah ya tsananta, kuma zatonku gareshi ya kyautata, to ku hada tsakaninsu, domin mutum kyakkyawan zatonsa ga ugangijinsa yana kasancewa ne gwargwadon tsoronsa ga ubangijinsa, kuma mutanen da suka fi kowa kyautata zato ga Allah, su ne suka fi kowa jin tsoron Allah.

Ka sani ya kai Muhammad dan Abubakar cewa ni na sanya ka jagoran mafi girman jama’a a guna mutanen Misira, kai ya cancanta ka saba wa son ranka, kuma ka kare addininka, kuma ko da ba ka da komai sai awa daya ta rage maka. Kada ka fusata Allah da neman yardar wani mutum daga halittunsa, domin Allah yana cike gurbin waninsa, amma babu wani mai cike gurbin Allah.

Ka yi salla a lokacin da aka sanya mata, kada ka gaggauta lokacinta don wani abu, kuma kada ka jinkirta ta daga lokacinta saboda shagaltuwa da wani abu, kuma ka sani cewa kowane abu na aikinka yana bin sallarka ne.
Ka sani jagoran shiriya da jagoran bata ba daidai suke ba, haka ma masoyin Annabi da makiyin Annabi ba daya suke ba, kuma Annabi (s.a.w) ya gaya mini cewa: Ni ba na ji wa al’ummata tsoron mumini ko mushriki; amma mumini imaninsa zai hana shi (cutar da ita), amma mushriki Allah zai rinjaye shi da ikonsa, sai dai ni ina ji muku tsoron duk wani munafukin boye, masani a harshensa, yana fadin abin da kuka sani, yana aikata abin da kuke ki” .

Muna ganin wannan nasiha ga jagoran da aka nada wa Misira ta isa ga dukkan mai hankali, kuma mun kawo dukan wasikar ne saboda muhimmancinta bai kebanta da jagora ba kawai, domin duk abin da aka kawo a ciki ya shafi kowane mutum mai neman tsira gobe kiyama.

Don haka yana daga cikin hakkin wanda ake jagoranta -dan kasa- a samar masa da aminci, da kariya, da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra’ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira.

Shugaba ya sanya alaka mai karfi tsakanin ma’aikatansa masu hidima ga al’umma da ita al’ummar kanta; misali akan samu tazara tsakanin masu tsaro da al’ummar kasa!. Samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al’umma, ta yadda al’umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon karancin wayewa da masu tsaro ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al’ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.

Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawa ko salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al’umma kuma ba sa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu.

Wani lokaci kamar suna cike da jin haushin mutane ne, da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi, mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.

Ban taba sanin cewa al’umma tana da tazara mai yawa da ‘yan doka ba sai ranar da na samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la’antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.

Kuma a nan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la’antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai ya ce: Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki. Ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.

A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin ‘yan sanda da al’umma, amma ra’ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al’ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al’ummarsa, sai ya cire wa al’umma jin cewa shi daga cikinta yake.

Haka al’amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa da samar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma duk da haka sai al’umma ba ta jin su nata ne haka su ma ba sa jin al’umma ta su ce. Da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin ba sa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja.
Rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, domin na sha jin soja (limami) yana nasiha a masallacin Barikin 44 da yake Kaduna yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri ‘ya’yansu? Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Haka nan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al’umma daban-daban ce a cikin al’umma daya.

Duba ka ga me Imam Ali (a.s) yake cewa game da mai tsaron kasa: “Runduna: Ita ce kariyar al’umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al’ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su” . A wani wurin yana cewa: “Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirri na gari (wato mai dabi’u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al’amuran al’umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, maras bayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar da shi . A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo ba wa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne a kan hukuma a ko’ina ne yake, al’amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.

Yana daga cikin hakkin dan kasa a samar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa. Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni sau da yawa maciya amanar al’umma suka sayar da su al’umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.

Game da Arzikin Kasa kuwa; sau da yawan talakawa ba sa ganin suna da hakki a arzikin kasa sai ‘yan kadan, al’amarin ya kai ga wasu masu tafiyar da al’amarin al’umma suna ganin hakan. Sau da yawa mai mulki ba ya kiyaye hakkin wanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa sai dai ka mutu da bakin ciki.

Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasar nan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan.
Sannan mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talaka yana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masu jin dadi ne.
Wani abin kunya da ‘yan kasarmu suke sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda suna jin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta.

Irin wannan al’amarin ya faru wata rana a tashar jiragen sama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Haka nan ake tara wa ‘yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.

Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma’auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne.
Wani lokaci akan ja shari’a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa.
Wani lokaci hakkin yana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu.

Wani lokaci kuma akan iya murgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.

Idan muka waiwayi garuruwa kuwa zamu ga Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da na al’umma yana daga cikin mummunan al’amari da ya addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko’ina ana iya zuba shara . Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kananan lunguna .
Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa da na motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.
Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami’ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko’ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi.

Sai na fara tunanin Jam’iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga can daga Jami’ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya a kan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsu ita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al’umma.
Ba ma jami’a ba, a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin. Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.
Sayar da hanyoyi don gini, sannan da za a rusa da su talakawan ne zasu tsine wa wanda ya rusa, alhalin shi wanda zai saya ya kamata ne ya fara zuwa ya ga taswirar gari, da kotu, da hukuma, domin ya tabbatar da ba hanya aka sayar masa ba, sai dai!…

In da rayuwa nan ga kadan za mu dora da ga in da muka tsaya insha Allah,

dan uwan ku a Musulnci Isiya Sy

Yi comment ko shere dan wasu su anfana.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Related Posts

Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share