RAYUWAR AUREN SAYYIDA FATIMA (A.S) | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→ Sayyida Fatima (As)RAYUWAR AUREN SAYYIDA FATIMA (A.S)

Post by , 8 months ago

Category: → Sayyida Fatima (As), 430 Views

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin qai.
Tsira Da Aminci Su Tabbata Ga Annabi Da Iyalan Gidansa Tsarkaka

Wannan rubutun namu zai magana ne a kan rayuwar aurenSayyida Fatima (a.s) da Imam Aliyu (a.s) wanda za mu yi shi takaitaccen kamar haka:

Neman Auren Sayyida Fatima (a.s) Kamar yadda kowa ya sani ne cewa a lokacin da ‘ya mace ta isa aure, sau da yawa takan sami manemi ko manema da sukan zo
domin su aure ta, to ita ma Sayyida Fatima (a.s) haka al’amarinta ya kasance, kamar yadda ya zo cewa daga cikin Sahabban Manzon Allah (s.a.w.a) akwai wadanda suka zama babban burinsu da abin alfahari a rayuwarsu shi ne su auri Sayyida Fatima (As).

An rawaito cewa daga cikin fitattun Sahabban akwai Abubakar da Umar, amma Manzon Allah (S) ya ce masu: “Al’amarin Fatima ba a hannuna yake ba, yana wajen Allah (T)”.

Bayan haka sai Mala’ika Jibirilu ya sauko zuwa wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce masa: “Ya Muhammad! Allah ya ce yana gai da kai, kuma ya ce: Ya daura auren Fatima da Aliyu, Allah ya zabi Aliyu ne saboda Fatima, kuma ya zabi Fatima ne saboda Aliyu”.

Imam Aliyu (a.s) shi ma yana daya daga cikin masu neman auren Sayyida Fatima, kuma Manzon Allah (s.a.w.a) saboda abin da aka ambata a baya na al’amarin auren sai ya aiwatar da umarnin da aka ba shi daga wajen Allah (T). A ruwayoyi masu yawa ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “In da babu Aliyu, to da Fatima ba ta da abokin hadin aure”. Saboda haka, bisa umarnin Allah (T) ne aka shirya bikin Fatima (As) da Imam Ali (a.s) kuma aka gudanar da shi.

Wannnan ke nan, amma ta fuskar sadakinta kuwa; abu ne sannane cewa wani abu ne wanda bai taka-kara-ya-karya ba (sabanin al’adar Larabawa kafin zuwan musulunci, domin kuwa sadakinsu ya kasance mai matuqar yawan gaske), kuma da wannan dan sadakin ne ta shiga cikin gidan nasa, kuma albarkacin wannan auren ne za mu ga gwalagwalen ‘ya’yaye guda biyar wadanda suka haskaka Duniya kuma su ne masu haskaka Lahira, kamar yadda za mu gani a cikin riwayoyi masu yawa daga Kakansu Manzon Allah (s.a.w.a); wato Imam Hasan, Imam Husaini, Zainab, Ummukulsum da Kuma Muhsin.

Yadda Rayuwarta Ta Kasance Tare Da Imam Ali (a.s) 

Lallai Sayyida Fatima (a.s) abar koyi ce ga dukkanin mata, kamar yadda za mu ga tsarin rayuwarta a wadannan nukutotin masu zuwa, wadanda rayuwarta da ta mijinta suka tafi a kansu:

1) Rayuwa irin ta talakawa da taka-tsantsan a kan rayuwar Duniya.

2) Taimakekeniya a cikin zaman takewar rayuwarta da mijinta.

3) Qimar aure da tafiyar da rayuwar auren bisa ingantacciyar zamantakewa.

4) Kulawa da baqi da karbarsu hannu bibbiyu ba tare da qyama ko hantara ba.

5) Infaqi da sadaukarwa a cikin zamantakewar aurensu ba tare da takurawa miji ba.

6) Yin Amfani da hanyoyin adddini da tarbiyyar addini wajen magance matsaloli.

7) Raba aikin gida tsakaninta da mijinta, ta yadda kowa ya tsayu da wazifarsa.

8) Girmama juna, saurarawa juna a cikin dukkanin bangarorin zamantakewa aurensu.

9) Tattaunawa da yin shawara da juna a wajen gudanar da al’amuran rayuwa.

10) Biyayya cikakkiya da miqa wuya ga miji ba tare da gajiyawa ko qosawa ba.

11) Yin kwalliya da tsaftace jiki da gida saboda kwantarwa miji hankali da faranta ransa.

12) Gina rayuwar iyali a kan jihadi da sadaukar da kai ga musulunci da musulmi.

13) Gidan Sayyida Fatima gida ne tsarkakakke wanda mala’iku suke dabdala a cikinsa.

14) Lura da halin akwai ko babun da miji yake ciki wajen neman abubuwan bukatun gida.

15) Rashin neman buqatun da suka shafi rayuwar duniya a wajen miji.

16) Kiyaye haqqin miji wajen tafiyar da rayuwar gida da iyali.

17) Haquri da jurewa wahalhalun da Imam Aliyu (a.s) ya sami kansa a cikinsu.

18) Tattaunawa da yin fira mai debe kewa tsakanita da mijinta.

To a dunqule dai wadannan su ne abubuwan da za mu iya gani kuma mu yi koyi da su a cikin rayuwar wannan baiwar Allah Tsarkakakkiya Zababbiya.

Da fatan Allah ya sa mu dace. Amin

Littattafan Da Aka Yi Amfani Da Su A Wannnan Maqalar

1- Sazemane Auqaf Wa Umuri Khairiyye, Fayame Yase Nabawi, Intisharate Auqaf, Bugun Shekara Ta 1392 sh, Tehran, Iran.

2- Mahadi Naili Pur, Farhange Fatimiyye, Bugun Pasdare Islam, Bugu Na 8, Shekara Ta 1389 sh, Isfahan, Iran.

Kuyi Comment Sannan Kuyi Shere dan wasu ma su anfana.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share