RAYUWAR FATIMA (AS) TARE DA MAHAIFANTA Da Mahaifiyar Ta | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→ Sayyida Fatima (As)RAYUWAR FATIMA (AS) TARE DA MAHAIFANTA Da Mahaifiyar Ta

Post by , 8 months ago

Category: → Sayyida Fatima (As), 408 Views

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah (t) wanda ya aiko Manzonsa Muhammad tsira da aminci su tabbata a gareshi da iyalan gidansa tsarkaka, kuma ya kara sanya Sayyida Zahara ta zamanto abin
koyi ga sisters kai har da maza.

To sanannen abu ne a gare mu cewa bayani kan ruyuwar Sayyida Fatima (a.s) tare da mahaifanta yana da yalwa da kuma fadin gaske, tamkar kogi ne da ba shi da iyaka, amma dai duk da haka za mu dan ce wani abu kadan don neman tabarruki.

Ita Sayyida Fatima (a.s) ta bude ido ne a gida mai tarin albarka, gidan annabta, gidan kaiwa-da-kawowar mala’iku. To don haka sai ya zamanto ta sami irin tarbiyyar Annabawa (a.s), kuma ta sami kyawawan dabi’u, kamar karamci da kamewa, hakan ya sa rayuwarta ta kasance mai tarin falala da albarka, wajen hidima ga
addinin musulunci da musulmi.

Kasantuwar cewa wannan maqalar za ta yi magana ne kawai a kan rayuwar Sayyida (a.s) tare da mahaifanta, wanda kuma ba zai ba mu damar shiga wasu bangarorin rayuwar tata ba, saboda haka za mu taqaita tsokaci a kan abubuwa kamar haka:

(1). Rayuwarta da mahaifiyarta.
(2). Rayuwarta da mahaifinta

Rayuwarta (As) Da Mahaifiyarta

Malaman tarihi sun bayyan cewa; Sayyida ba ta sami tsawon rayuwa tare da mahaifiyarta ba, to amma cikin hikimar ubangiji da ya so ya bayyana karamomin Sayyida (a.s), sai ya sanya ta ta kasance mai debewa mahaifiyarta (Sayyida Kadija (a.s)) kewa tun tana ciki, lokacin da matan Makka suka guje ta saboda auren da ta yi da Manzon Allah (s.a.w.a), wanda tarihi ya tabbatar da cewa a lokacin da Sayyida Kadija (a.s) take xauke da cikin
Sayyida Fatima (a.s) ta kasance tana hira da ita, wanda hakan  yana samar mata nutsuwa, kwanciyar hankali, da rashin buqatuwa zuwa ga sauran matan Quraishawa baki-xaya.

Haka kuma, duk da qarancin shekarunta ba ta gushe ba tana mai daukewa mahaifiyarta kewa da tayata ayyukan gida (kamar yadda ‘ya’ya mata suke taya mahaifansu aikace-aikacen gida) har
zuwa lokacin da Allah (t) ya karbi rayuwar mahaifiyar tata.

Rayuwarta (a.s) Da Mahaifinta

Bayan an haifi Sayyida (a.s) da wadansu ‘yan shekaru kadan, Allah (t) ya karbi rayuwar mahaifiyarta kafin hijirar Manzon Allah (s.a.w.a) zuwa garin Madina, wannan shekarar da aka karbi
Sayyida Kadija malaman tarihi na kiranta da (Amul Huzni) wato shekarar bakin ciki da juyayi. Sayyida Zahra (a.s) a cikin wannan ‘yar muddar ta zauna da mahaifinta ne su biyu kawai, to a wannan zaman da suka yi Sayyida Faxima (a.s) ta nuna gwarzantaka da qoqari sosai ta
vangaren taimakawa mahaifinta, ta yadda ta yi qoqarin ta ga ta yi masa hidimar da mahaifiya kewa danta, wanda har ta kai
mahaifin nata ya yi mata laqabi da (Ummu Abiha), kuma yana matuqar nuna mata qaunar da babu wani mahaifi da yake yi wa diyarsa irinta a doron qasa .

domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa duk lokacin da Sayyida (a.s) ta kamo-hanya za ta zo wajen da Annabi yake, sai ya tashi yana mai tarbarta da lale marhabin, haka nan ita ma take yi masa idan ya ziyarce ta.

Bisa wadannan abubuwan da wadanda ma ba mu ambace su ba, za mu iya fahimtar irin qwaqqwarar ala’qar da take tsakanin Sayyida Fatima (a.s) da mahaifanta.

Darussan Da Suke A CikinMaqalar A Taqaice

1. Yadda ya kamata ‘iyaye su yi mu’amala da ‘ya’yansu maza ko mata .

2. Muhimmancin iyaye da yadda ake kula da su koda kuwa ba su manyanta ba .

3. Rawar da ‘ya‘ya za su taka wajen samar da natsuwa da kwanciyar hankali ga iyayansu.

Littatafan Da Aka yiAmfani Da Su A WannanMaqalar

1. Rasuly, Sayyid Hashim, Zandageye Hazarati Fatime, Bugun Tehran: Daftari Nashri Farhangiye Islamy, Bugu Na 8, Shekara Ta 1386.

2. Ridhwa’ny, Aliyu Asghar, Fatime Zahra Mazlumiye Tarikh, Bugun Subhu Ameedya’ra’n, Bugu Na 1.

Kuyi Comment Sannan Kuyi Shere dan wasu ma su anfana.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share