TSORO DA JUYAWA DA BAYA | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→AshuraTSORO DA JUYAWA DA BAYA

Post by , 7 months ago

Category: →Ashura, 199 Views

Kwana guda da samun wannan wasika ta Yazid bn Mu’awiyya, sai Ubaidullah bn Ziyad ya kama hanyar Kufa zuciyarsa cike da fushi da mugunta, su kuwa mutanen Kufa suna nan cikin shirin tarbar Imam Husaini (a.s) duk kuwa da cewa da dama daga cikinsu ba su ma taba gani ko haduwa da Husain (a.s) din ba. Don haka sai Ibn Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya boye kansa ya shigo cikin garin sanye da bakin rawani ya kuma rufe fuskansa.

Koda ya shigo garin sai ya dinga zagawa tituna-tituna na garin, su kuwa mutane (suna zaton Husain ne) sai suka fito suna ta masa barka da zuwa da kuma gaishe shi, suna cewa: “Amincin Allah ta tabbata a gare ka Ya Dan Manzon Allah(1)”.

Cikin fushi da bakin cikin kan abin da ya gani daga mutanen Kufa suna zaton Husain (a.s) ne, sai ya kama hanya zuwa fadar mulkin garin. Wannan abin da ya gani dai ya ishe shi shaida kan irin kaunar da mutanen Kufa suke wa Husaini (a.s) da kuma gabarsu ga Yazid da hukumarsa. To amma daya daga cikin masu masa rakiya mai suna Muslim bn Amru al-Bahili don kokarin razana mutane da kuma sanya tsoro cikin zukatansu, sai ya yi tsawa yana mai ce wa jama’a: “Ku kauce, wannan gwamna Ubaidullah bn Ziyad ne(2)”.

Ubaidullah bn Ziyad kuwa ya ci gaba da tafiya zuwa fadar mulki alhali jama’a kuwa suna binsa suna zaton Husaini (a.s) ne saboda yaudararsu da ya yi. A waje guda kuma Nu’umanu bn Bashir, gwamnan Kufa wanda shi ma yake cikin damuwa da kuma tunanin cewa Imam Husaini (a.s) ne yake zuwa (bai san cewa Ubaidullah bn Ziyad ba ne), sai ya leko daga fadar tasa yana cewa: “Ina hada ka da Allah da ka bar wannan guri, wallahi ba a shirye nake in bar maka wannan mukami nawa ba, haka nan kuma ba ni da niyyar yakanka(3)”.

Ibn Ziyad dai bai ce masa komai ba sai nufan kofar fadar ya ke yi shi kuma Nu’uman yana ci gaba da kallonsa, lokacin da ya fahimce cewa ba wani ba ne face Ibn Ziyad sai ya sa aka bude masa kofa, shi kuwa ya shiga ya kwana a gidan. Al’ummar garin Kufa dai suka ci gaba da zama cikin yanayin zullumi da tsoro saboda faruwar wannan lamari.

Da gari ya waye sai Ibn Ziyad ya mike yana mai gabatar da jawabi ga al’umma wadanda suka taru don salla, a yayin jawabin nasa dai Ibn Ziyad ya yi alkawarin saka wa duk wadanda suka yi biyayya (ga hukumar Yazid) da aminci da kuma rayuwa ba tare da tsangwama ba, sannan kuma ya yi barazanar azabtar da duk wani wanda ya yi kokarin yin bore da kuma adawa da hukumar har inda yake cewa: “Zan yi amfani da bulaliya da takobina a kan duk wani wanda ya saba wa umarnina da kuma nuna rashin amincewa da shugabancina(4)”.

Daga nan sai ya tilasta wa wadanda suke wajen aikin leken asiri don bincikowa da kuma kawo masa rahoton kan abin da ke gudana da kuma masu adawa da hukama, yana mai barazanar azabtar da duk wanda ya ki aikata hakan da kuma hana shi albashin da ake bai wa mutane, yana mai cewa:

“Duk wani wanda ya kawo mana labari kan masu adawan to ya tsira daga cutarwa, amma duk wani daga cikinku da ya ki ba da hadin kai to dole ne ya lamunce mana cewa babu wani daga cikin zuriyarsa da zai saba mana ko kuma cutar da mu. Duk kuwa wanda ya ki aikata haka to kuwa ba shi da aminci kuma jini da dukiyarsa sun halalta mu zubar da su. Duk wani mai unguwar da aka samu wani masoyin Husaini a cikin unguwarsa alhali kuma ya ki ya sanar da mu, to za a tsire shi a bakin kofar gidansa kuma za a hana albashin da ake ba wa mutanensa(5)”.

To fa daga nan ne lamurra suka fara sake zani, yanayi ya fara canzawa da dauka shakali na daban, tsoro da fargaba suka fara shiga zukatan mutanen Kufa da shuwagabanninsu. A bangare guda kuma, hukumar Ubaidullah bn Ziyad ta fara kafa tubalinta da kuma samun gindin zama, ta hanyar tsoratar da mutane da hanyoyi daban-daban da ta samu da kuma amfani da kudi da cin hanci ga ‘yan leken asirinta wadanda su kuma suke ci gaba da yada labarurruka na tsoratarwa da ta da hankulan al’umma. Ta haka ne kuma al’umma suka fara gudu da kuma janyewa Muslim bn Akil, manzo kana kuma wakilin Imam Husaini (a.s), lamarin da ya tilasta masa sake tunani da kuma canza salon yadda yake gudanar da ayyukansa, inda ya yi kaura daga gidan Mukhtar bn Ubaidah al-Thakafi zuwa gidan daya daga cikin sanannun shuwagabannin mutanen Kufa kuma mabiyin Ahlulbaiti (a.s) wato Hani bn Urwah, ya ci gaba da zama a can a boye ba tare da kowa ya san inda ya ke ba. To amma dai daga baya sai da ‘yan leken asirin hukuma suka gano inda ya ke, kana kuma suka kai labari.

Jin haka sai Ubaidullah bn Ziyad ya kira Hani bn Urwah fadarsa ta yadda ba za a yi tunanin ko akwai wani abin da ya faru ba, ya aika masa kan ya zo su tattauna tsakaninsu don magance wasu matsalolin da suka taso. To amma shigan Hani fadar ke da wuya sai kawai ya gan shi a gaban kotu ana tuhumarsa, ga ‘yan leken asiri kuma suna shaidawa kan cewa shi yana daga cikin mabiya Imam Husaini (a.s), yana kuma shirya gagarumin yunkuri na yin bore wa hukuma da kuma tara kudade, makamai da jama’a ga Imam Husaini don yin bore wa hukuma sannan kuma ya boye Muslim bn Akil a gidansa. Hani dai ya yi kokarin musanta hakan da kuma kare kansa, to sai dai kuma Ubaidullah bn Ziyad ya fada masa da duka a fuskarsa da kuma zubar masa da jini, ya yi kokarin kare kansa da kuma mayar da martani ga Ubaidullah bn Ziyad din to amma an ce wai sarkin yawa ya fi sarkin karfi, nan take jami’an tsaron da ke gurin suka ci karfinsa suka kama shi. Daga nan sai Ibn Ziyad ya ba da umarnin a rufe shi a daya daga cikin dakunan gidan.

Ko da labarin kama Hani ya fito, sai ‘yan kabilarsa suka taru a kofar fada suna kira da a sako shi, to amma sai Ubaidullah ya yi amfani da wata hanya ta makirci ya tura Alkali Shurayh da ya fita zuwa gare su da bayyana musu cewa ba kama Hani a ka yi ba suna tattaunawa ne da sarki kan matsalolin al’umma kuma nan ba da jimawa ba zai fito, ta haka ne jama’an suka watse kuma aka kawo karshen wannan bore na ‘yan kabilar Hani.

Garin Kufa dai ya shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali da kuma zubar da jini tsakanin bangarori biyu. Labarai kala-kala kuwa sai yaduwa suke yi tsakanin al’umma da kuma batun kama Hani da dai sauransu, a waje guda kuma ‘yan leken asiri suna nan suna ta yada labarin cewa nan ba da jimawa wasu sojoji za su iso daga Sham (Siriya) don murkushe wannan bore da kuma azabtar da Muslim bn Akil da mabiyansa. A takaice dai tsoro, fargaba da rauni sai suka fara shiga zukatan masu yunkurin da kuma haifar da gibi a tsakanin wannan harka ta yunkuri da kawo canji.

A cikin irin wannan hali da ake ciki dai, Muslim bn Akil yana nan a boye yana darasin yadda lamurra suke gudana. Daga karshe dai ya kuduri aniyar tara jama’arsa don kai hari kan fadar sarki da kuma kawo karshen hukumar Ibn Ziyad din. Don haka sai ya tara mutanensa da suka riga suka yi masa bai’a da kuma alkawarin kasancewa tare da shi(6), inda suka kai hari ga fadar mukin(7). Da farko dai mutanen Ibn Akil suna samun nasara a kan mutanen Ibn Ziyad, lamarin da ya tilasta masa gudu cikin gida tare da mutanensa da kuma rufe kofofin fadar gaba dayansu. To amma sai Ibn Ziyad ya turo mutanensa (‘yan leken asiri) cikin mutanen Muslim bn Akil a boye suna masu kira da a kiyaye tsaron lafiyar mutane da kuma tsoron zubar da jini, a bangare guda kuma suna razanar da mutane kan cewa lallai fa akwai wasu sojoji marasa imani da suke kan hanyar isowa Kufan daga Sham. Duk hakan kuwa suna yi da nufin jan lokaci da kuma rarraba kan mutanen Muslim bn Akil din. Haka dai lamarin ya ci gaba, da sannun-sannu mutane kuwa suna gudu da sahu suna barinsa, har lokacin da wuri ya yi duhu sai ya kasance babu kowa tare da shi in ban da mutane goma wadanda suka shiga masallaci tare da shi don yin salla, alhali kuwa da farko sun kai kimanin mutane dubu hudu.

To lokacin da Muslim ya gama sallar mangariba, juyowansa ke da wuya sai ya ga babu kowa tare da shi, babu wani mutum guda wanda zai shiryar da shi hanya ko kuma ya ba shi mafaka a wannan gari da ba garinsa ba. Ta haka ne Muslim ya zauna shi kadai a cikin masallacin Kufa bai san inda zai je ba kuma ba shi da wani wanda zai taimaka masa ko kuma kula da shi.

Babu shakka wannan yanayi ne mai tada hankali da kuma raunana zuciya da ke bukatuwa da jarumin shugaba mai karfin zuciya wanda zai iya daure wa hakan. Haka dai Muslim ya fuskanci wannan sabon canji da karfin gwuiwa da kuma zuciyar da ba za taba mika wuya ba, ya fito yana ta yawo a kan titunan garin Kufan ko zai sami wata mafita, ko kuma ya sami hanyar da zai fice daga garin kafin a kama shi don ya samu damar isa zuwa ga Husaini (a.s), wanda ya ke kan hanyarsa ta zuwa Kufa, don sanar da shi halin da ake ciki da kuma hana shi isowa.

Haka dai Muslim ya ci gaba da yawo a kan tituna da lungunan garin Kufa da suka kasance tsit saboda tsoro da fargaba, a bangare guda kuma ga shi an baza jami’an tsaro da ‘yan leken asiri don kamo wakili kana kuma manzon Imam Husaini (a.s) wato Muslim bn Akil. Yana cikin tafiya sai ya kai ga wani gida da wata mace take tsaye a kofarsa mai suna Taw’a, sai ya tsaya a kofar gidan cikin damuwa da jin kunya, ya bukace ta da ta taimaka masa da ruwan sha, ta shiga ta kawo masa ruwan. Bayan da ya sha ruwan sai kuma ya zauna a bakin kofar, cikin damuwa bai san inda zai je ba.

A tattare da shi dai ga alamu na wahala da bakunta, wannan zama da ya yi a bakin kofar sai ya janyo hankalin wannan mata, inda ta matso kusa da shi ta ce masa; a a ashe ba ka gama shan ruwan ba? To shin ba za ka tafi gidanka ba? Sai ya amsa mata da ce shi bako ne ba shi da gida kuma ba shi da iyalai a wannan gari, daga nan sai ya bayyana mata ko shi wane ne: “Ni ne Muslim bn Akil bn Abi Talib, wakilin Husaini kana kuma manzonsa ga mutanen Kufa, kuma dan Baffansa”. Nan take sai ta bude masa kofa ta shigar da shi gidan don ya kwana a ciki daga baya kuma a ga mai zai faru gobe(8).

To sai dai kuma a daidai wannan lokaci shi kuma Ibn Ziyad ya fara motsawa saboda ganin irin abin da ya faru ga Muslim bn Akil bayan sallar magariba, don haka sai ya umarci mai kiran salla da ya kira salla ya kuma shaida wa jama’a cewa:

“Babu aminci ga duk wani daga cikin jami’an tsaro, shuwagabannin al’umma, mabiya da mayaka da ya yi sallar dare ba a wannan masallaci ba(9)”.

Haka dai kusan dukkan al’umma suka amsa wannan kira saboda tsoro da fargaba wasu kuma ta hanyar rashawa da cin hanci, inda suka cika masallacin makil. Daga nan sai Ibn Ziyad ya ja su sallar Lisha, sannan ya mike don yi jawabi wa mutane yana mai musu alkawura da kuma yi musu baraza, da kuma cin mutumcin Ibn Akil kwarai da gaske, ga kadan daga cikin abin da ya ce:

“Bayan haka, wannan jahili wawa Ibn Akil ya yi kokarin ta da hankali da kuma haifar da sabani kamar yadda dai kuka gani, don haka babu wani aminci na Ubangiji ga mutumin da muka same shi a gidansa. Duk wanda ya kawo shi yana da lada na jininsa, ku ji tsoron Allah Ya ku bayin Allah sannan kuma ku kula da biyayya da kuma mubaya’arku. Kada ku aikata wani abin da zai kasance cutarwa gare ku.

Ya Husayn bn Numayr(10), mahaifiyarka za ta yi rashinka matukar dai aka bude duk wata kofa daga kofofin lungunan Kufa ko kuma wannan mutumin ya fito amma ba ka kawo min shi ba. Na ba ka izini kan gidajen mutanen Kufa, ka tura masu bincike don binciken mutane a kan hanyoyi, haka nan kuma gobe da safe ka fitar da mutane daga gidajensu, ka bincike su sosai don ka kawo min wannan mutumin(11)”.

Ta haka ne dai Ibn Ziyad ya bayar da wannan umarni nasa da kuma bincike gida-gida don nemo Muslim bn Akil da kuma kama shi alhali kuwa yana nan a boye a gidan wannan muminan mace (Taw’a) yana jiran samun damar fita ko kuma kulla alaka da wani mutum wanda zai taimaka masa kan wannan aiki da ya sa a gaba.

Ta haka ne dai Ibn Ziyad ya bayar da wannan umarni nasa da kuma bincike gida-gida don nemo Muslim bn Akil da kuma kama shi alhali kuwa yana nan a boye a gidan wannan muminan mace (Taw’a) yana jiran samun damar fita ko kuma kulla alaka da wani mutum wanda zai taimaka masa kan wannan aiki da ya sa a gaba.

To sai dai kuma kaddara ta gitta, don kuwa dan wannan mata ya gano inda Muslim din yake boye, don haka da gari ya waye sai ya garzaya wajen Ibn Ziyad don ba shi wannan labari, yana mai tsoro da kuma kwadayin samun kyautar da aka ce za a ba wa duk wanda ya kawo labarin inda Muslim din ya ke. Don haka nan take sai Ibn Ziyad ya turo ‘yan sandansa guda saba’in don bincike da kuma kame Muslim din.

Ko da Muslim ya ji sautin kofatun dawaki da kuma ihun da wadannan ‘yan sanda suke yi, sai ya yi shirin yaki don fuskantarsu. Daga nan sai suka balle kofar gidan suka shigo, amma Muslim dai bai mika kai ba, inda ya fuskance su da yaki, irin wannan jarunta tasa ta sanya su komawa da baya da kuma ficewa daga gidan.

To bayan da suka ga ba za su iya da shi ba, sai suka bullo masa da wata dabara kuma ta daban, inda suka dinga jefo masa duwatsu da kuma itatuwa dauke da wuta a jikinsu, lamarin da ya tilasta masa ficewa daga gidan da kuma tsayawa a waje amma duk hakan dai yana rike da makaminsa a hannu, duk da cewa sun ji masa raunuka a jikinsa, jini na zuba ko ta ina. Daga nan sai suka fito da wata dabarar kuma suka ce masa: ‘Kana cikin aminci kada ka kashe kanka’. Daga baya Muslim ya yarda da wannan kira na su, inda suka tafi da shi zuwa fadar mulki, to sai dai kuma tun kafin nan ma dai sun karya wannan alkawari na su, suka kwace takobin da ke hannunsa da kuma ci gaba da ci masa mutumci.

Daga nan sai suka shiga da shi fadar mulkin wurin Ibn Ziyad, koda shigansu sai Muslim ya ki gaida Ibn Ziyad kamar yadda ake masa, ya tsaya a gabansa kamar sandararren tubali wanda duk rintsi ba ya girgizuwa. Mutanen biyu dai sun ta mayar da maganganu masu zafi ga junansu, inda lamarin ya kawo karshe da fadin Ibn Ziyad cewa: “Kai macacce ne”, sai Muslim ya amsa masa da cewa: “To amma ina son ka ba ni damar yin wasiyya.

Ibn Ziyad ya amince da hakan, sai Muslim ya bukaci Umar bn Sa’ad da ya rubuta wasiyyar da kuma kiyaye ta saboda alaka ta jini da take tsakaninsu. A cikin wannan wasiyya dai, Muslim ya yi wasicci ne da abubuwa uku(12). Bayan gama rubuta wannan wasiyya wanda aka yi a wani sashi na fadar Ibn Ziyad sai Umar bn Sa’ad ya komo cikin fadar yana bayyanar da abin da wasiyyar ta kumsa yana izgili da ita.

Ibn Ziyad ya ci gaba da barazana wa Muslim da kuma ci masa mutumci da zage-zage da dai sauransu, shi kuwa Muslim yana mayar masa da martani cikin jaruntaka ba tare da nuna tsoro ko damuwa ba. A bangare guda kuma babu wani wanda ya cika wannan alkawari na aminci da suka yi wa Muslim, don Ibn Ziyad ba shi da nufin barin Muslim a raye, ganin ya zo Kufa ne don fuskantar mulkinsa da kuma ganin bayansa, to a halin yanzu kuwa ga shi ya sami damar huce fushinsa a kansa.

Daga nan sai Ibn Ziyad ya umarci sojojinsa da su hau da Muslim kololuwar fadar, ya kuma ce wa Bakr bn Hamran, wanda daman Muslim ya ji masa rauni mai girman gaske: ‘Karbi wannan takobin ka sare kansa, sannan kuma ka turo jikinsa da kan nasa kasa. Daga nan sai suka daure Muslim suka haura da shi kan soron yana fadin Allahu Akbar da kuma tsarkake Ubangiji don shirin gamuwa da wannan daraja mai girma ta shahada.

Bayan hawansu wannan gini, sai suka fille kan Muslim(13), inda ya samu nasarar shiga tawagar shahidai, muminai, Annabawa da kuma salihan bayi. Daga nan kuma sai sojojin Ibn Ziyad suka kamo Hani bn Urwah suka daure hannayensa suka nufi kasuwan dabbobi da shi, inda bayan sun kashe shi da kuma gutsure kansa, sai suka hada kawukan biyu suka aika da su zuwa Sham wurin Yazid bn Mu’awiyya. Jikkunan kuwa sai suka daure su suna jan su cikin tituna da kasuwan garin Kufan.

Ta haka ne dai aka kawo karshen wannan yunkuri na garin Kufa, wanda ya bude babban shafi cikin tarihi, kana kuma ya haifar da gagarumin yunkuri a nan gaba don rayar da Musulunci da kuma kawo canji da shiriya.


(1)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk/ Dabari, juzu’i na 4, shafi na 258.
(2)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 206.
(3)- Kamar na sama
(4)- Kamar na sama.
(5)- Kamar na sama shari na 207.
(6)- Sayyid Ibn Dawus ya bayyana cewa an yi gumurzu tsakanin mutanen Muslim da mutanen Ubaidullah bn Ziyad, dubi littafin Maktal al-Husain as na Sayyid Ibn Dawus, shafi na 22.
(7)- Sayyid Ibn Dawus ya ce: “Lokacin da dare ya yi sai mutanen Muslim suka fara gudu suna rabuwa da shi suna ce ma junansu: Me za mu yi da gagauta zuwan fitina, ya kamata mu kasance cikin gidajenmu mu zuba ido wa wadannan al’umma har Allah Ya shirya tsakaninsu’. Babu wanda ya saura tare da shi in ban da mutane goma, su din ma sun gudu sun bar shi lokacin da aka shiga sallar mangariba”. Dubi littafin Maktal al-Husain as na Sayyid Ibn Dawus, shafi na 22.
(8)- Dabari ya ruwaito wannan labari cikin littafinsa Al-Umam wa al-Muluk, juzu’i na 4, shafi na 277.
(9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 213 da kuma al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu’i na 4, shafi na 278.
(10)- Husayn bn Numayr shi ne shugaban ‘yan sandan Kufa.
(11)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 213 da kuma al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu’i na 4, shafi na 279.
(12)- Daga cikin abin da ya yi wasiyya din har da ya sayar da takobi da garkuwarsa don biyan bashin da ke kansa.
(13)- Muslim bn Akil da Hani bn Urwah sun yi shahada ne a garin Kufa a ranar Laraba 9 ga watan Zil Hajji, shekara 60 B.H., kuma kabarin kowani guda daga cikinsu yana nan a Kufa, kowace rana dubban al’umma ne suke kai musu ziyara.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share