ME YA SA IMAM HUSSAIN (AS) WANNAN YUNKURI KAWAI?! | 5Five Stars Media Sound

Barka Da Zuwa

Home

Downloads

English Side

Our Side Branch

Home→AshuraME YA SA IMAM HUSSAIN (AS) WANNAN YUNKURI KAWAI?!

Post by , 7 months ago

Category: →Ashura, 236 Views

Don amsa wannan tambaya mai muhimmanci, yana da kyau da farko mu yi dubi cikin wadannan abubuwa:

Na farko dai: Yazidu dan Mu’awiyya ya dare karagar mulkin al’ummar musulmi, wanda a fili yake bai cancanci hakan ba face ma dai hakan wani babban hatsari ne ga makomar al’ummar. Yazid dai fasiki ne wanda bai sami komi kashin tarbiyya irin ta Musulunci ba, don kuwa ya girma ne a gidan da hasken rana ta shiriya ta Musulunci ba ta taba bulla a cikinsa ba, don haka ba abin mamaki ba ne irin har tarihi ya nakalto mana cewa Yazid dan giya ne, dan caca da dai sauran munanan ayyuka da suka saba wa dokoki da ka’idojin Musulunci(1).

To amma duk da irin wannan hali da yanayi na Yazid, sai ga shi ya dare karagar jagoranci lamurran al’umma!!!

Wannan yanayi dai shi ne ya ba da dama ga duk wani yin karen tsaye ga sakon Musulunci da dokokinsa ya samu gindin zama, duk kuwa da cewa masu fatan alheri wa sakon – karkashin jagorancin Imam Husaini – sun yi amfani da wannan dama wajen kira da kuma jan hankulan mutane zuwa ga koyarwa ta hakika ta Musulunci. Don tuni al’ummar ta fara gano irin yanayin Yazid wanda ya saba wa koyarwa irin ta Musulunci, don haka ba su yi wata-wata ba wajen karban wannan kira. Kai hatta ma lokacin da dakarun Umayyawa karkashin jagoranci Hur bn Yazid al-Riyahi(2)suka kewaye Husaini (a.s) a kasar Iraki, shi ya kasance mai kira da kuma jawo hankulansu zuwa irin kauce wa hanya da sarakunan Umayyawan suka yi, inda yake cewa:

“Ya ku mutane! Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Duk wanda ya ga ja’irin sarki, mai halalta abin da Allah Ya haramta, mai saba alkawarin Allah, mai yin karen tsaye ga sunnar Ma’aikin Allah (s.a.w.a), mai cutar da bayin Allah, to amma sai bai yi kokarin canza shi ba a aikace ko kuma da baki ba, to lalle ne Allah Zai shigar da shi makomarsa (makomar wannan sarki ja’iri). Ku sani fa wadannan (sarakuna) sun tilasta yin da’a wa shaidan, kana kuma suka bar da’a wa Ubangiji, suna bayyanar da fasadi, suna wuce haddi, suna halalta abubuwan da Allah Ya haramta kana kuma suna haramta abin da Ya halalta”.

Ta hanyar wannan huduba da ma wasunta, Imam Husaini (a.s) ya bayyanar da hakikanin yanayin gwam-natin Umayyawa, motsa zukatan al’umma da kuma kawar da kurar da ta rufe musu gaskiya.

Na biyu: Irin yanayin al’ummar wancan lokacin yanayi ne na zaman dirshan da babu wani kokari da yake yi wajen fuskantar mummunan yanayi sabo da kauce wa hanya da ake ciki, hakan kuwa ya biyo bayan irin son jin dadi da kuma son kan da ke tattare da al’ummar ne, bugu da kari kan rashin ruhin tabbatar da abin da zai amfani al’umma gaba daya. Irin wannan yanayi ne ya sa manyan jagororin al’ummar suka debi makudan kudaden al’umma da amfani da su don amfanuwar kansu kawai(3).

Hakika idan har masu fadi a ji sun mai da hankali wajen sace dukiyar al’umma da neman riba, to ita ma kanta al’ummar ta nuna kanta a matsayin mai son duniyar, mai son tabbatuwa cikin jin dadin duniya da kuma guje wa duk wani kokari wajen fitar da kanta daga cikin irin wannan mummunan hali da take ciki.

Hakika idan har masu fadi a ji sun mai da hankali wajen sace dukiyar al’umma da neman riba, to ita ma kanta al’ummar ta nuna kanta a matsayin mai son duniyar, mai son tabbatuwa cikin jin dadin duniya da kuma guje wa duk wani kokari wajen fitar da kanta daga cikin irin wannan mummunan hali da take ciki.

A saboda haka ne ma watakila ba zai zamanto abin mamaki ba idan muka ga wasu daga cikin manyan musulmi suna kiran Imam Husaini – a lokacin da ya sanar da kudurinsa na fuskantar Yazid – da ya guje wa fuskantar gwamnatin Umayyawan. Saboda tsoron da ke cikin zuciyarsu da kuma masaniyar da suke da ita na kauce wa hanya da Umayyawa suka yi don haka suna ganin za a kashe shi ne kawai. A matsayin misali Umar al-Atraf ya ce masa: ‘Abu Muhammad al-Hasan ya gaya min cewa babansa Amirul Muminina ya gaya masa cewa za a kashe ka, don haka da za ka yi mubaya’a (wa Yazid) ai da shi ya fi maka alheri’.

Kamar yadda Abdullah bn Umar bn al-Khattab da Abdullah bn Zubair ma suka shawarce shi da kada ya fuskanci gwamnatin Umayyawan, da dai sauran al’umma(4)”.

Wannan dai kadan kenan daga cikin irin halin rashin ruhi na yunkuri da ke cikin zukatan da dama daga cikin shuwagabannin musulmi, kamar yadda kuma irin wannan yanayi da kuma tsoro suka mamaye zukatan sauran al’umma. Misali mutanen Kufa, duk da irin wasiku da kuma alkawarin da suka yi na taimakon Imam Husaini (a.s) da kuma fada da zalunci da ta’addanci da mahukunta karkashin jagoranci Ibn Ziyad, to amma duk sun mance da hakan, inda saboda son duniya da kuma alkawurran da aka musu suka koma bangaren Umayyawa suka bar Imam Husaini (a.s). Watakila abin da zai tabbatar mana da irin wannan yanayi na mutanen Kufa, shi ne amsar da Farazdak ya bai wa Imam Husaini (a.s) lokacin da ya tambaye shi yanayin mutane a Kufan, sai ya ce masa: “Zukatansu suna tare da kai, amma takubbansu suna tare da Banu Umayya”. Wannan yanayi dai yana nuna mana irin nauyin da wadannan mutane suke da shi a gaban Allah, kana kuma babban abin da ke nuna mana misali na munafuncin al’umma wanda ya samo asali daga irin bakar siyasar Umayyawa da ke kashe lamirin mutane.

Hakika wadannan abubuwa dai suna daga cikin dalilan da suka sa aka kaddamar da wannan yunkuri mai albarka, don rayar da macaccen lamiri, da ba abin da yake ganin in ban da son duniya da kuma rayuwa. Don kuwa Imam (a.s) ya riga da ya san cewa irin wannan yanayi mai ban haushi da al’ummar suke ciki a wancan lokacin ba shi da wata mafita ta shari’a ta kowani bangare, face ma dai shari’ar ce da kanta take kiran al’umma da su tsamar da kansu daga cikin duk wani yanayi da ba a gudanar da adalci da shiriya a cikinsa ba. Wannan yanayi da ya dauki son duniya da rayuwa a matsayin manufa da hadafi, kuma wanda a wurare da dama kuma Musulunci ya yi maganganu akansa cikin Littafin Allah mai tsarki:

يا أيُّها الذينَ امَنُوا مالكُمْ إذا قِيلَ لكُمْ انْفِروا في سبيلِ اللهِ اثَّاقَلْتُمْ إلى الأَرْضِ أَرَضِيتُم بالحياةِ الدُنيا مِنَ الاخِرةِ فما مَتَاعُ الحياةِ الدُنيا في الاخِرةِ إلاَّ قَلِيلٌ. إلاَّ تَنْفِرُوا يُعَذِّبْكُمْ عذابًا أليمًا ويَسْتَبْدِلْ قومًاغيْرَكُمْ ولاتَضُرُّوهُ شيئًا واللهُ علىكلِّ شيء قدير

“Ya ku wadanda suka yi imani! Me ya same ku , idan an ce muku, “Ku fita da yaki a cikin hanyar Allah”, sai ku yi nauyi zuwa ga kasa. Shin kun yarda da rayuwar duniya ne daga ta Lahira? To jin dadin rayuwar duniya bai zama ba a cikin Lahira, face kadan. Idan ba ku fita da yaki ba, Allah zai azabta ku da azaba mai radadi, kuma Ya musanya wasu mutane, wasunku (a maimakonku). Kuma ba za ku cutar da Shi da kome ba. Kuma Allah a kan dukkan kome Mai ikon yi ne”. (Suratut Tauba; 9: 38-39).

Haka nan kuma komawa zuwa ga azzalumai lamari ne abin ki:

(ولاتَرْكَنُوا إلى الّذينَ ظَلَموا فَتَمَسَّكُم النّارُ) “Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci har wuta ta shafe ku…”. (Suratu Hud; 11:113).

A wani wajen kuma Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

( إِنَّ اللهَ اشترى مِنَ المؤمنينَ أنْفُسهُمْ وأَمْوالَهمْ بأنَّ لهُم الجنّةَ, يُقاتِلونَ في سبيلِ اللهِ فيَقْتُلُون وَيُقْتَلونَ وعدًاعليه حقًّ )

“Lalle ne, Allah Ya saya daga muminai, rayukansu da dukiyoyinsu, da cewa suna da Aljanna, suna yin yaki a cikin hanyar Allah, saboda haka suna kashewa ana kashe su, (Allah Ya yi) wa’adi a kanSa, tabbatacce…”. (Suratut Tauba; 9:111).

To bisa wannan fahimta da Imam Husaini (a.s) ya yi wa wannan sako na Musulunci – wanda shi ne asalin hakikanin addinin Allah a aikace – ya sa ya bayyanar da rashin amincewarsa a fili kan irin yadda al’amurra suke gudana a wancan lokaci.

Haka nan kuma saboda irin masaniyyar da Imam Husaini (a.s) ya ke da shi kan nauyin da ya hau kansa da kuma ingancin wannan tafarki da ya dauka, ba abin mamaki ba ne idan aka ga ya kira mutane da na kusa da shi zuwa bangarensa da kuma riko da wannan tafarki wanda shi ne tafarkin Musuluncin da Allah Madaukakin Sarki ya yarje wa bayinsa masu gaskiya. Kamar yadda ya yi wa Abdullahi bn Umar yayin da ya kiraye shi da ya canza ra’ayinsa na kaddamar da jihadi akan Umayyawa, lokacin da ya ce masa: “Ka ji tsoron Allah, Ya Aba Abdarrahman, kada ka yi kasa a gwuiwa wajen taimakona”.

Ta haka ne Imam Husaini (a.s) ya fito da dukkan karfinsa don keta duhun da ya yi shamaki ga mahangar sakon Musulunci da kuma kashe lamiran zukata cikin tsawon lokaci, ya kuma lalata ruhin jihadi a tsakanin al’umma don ba wa azzaluman shuwagabanni ‘yan mulkin kama karya damar cin karensu babu babbaka. Haka nan kuma don wanke tunanin al’umma wanda yake cike da kurar bakar siyasar masu mulki wacce ta dare da kuma rufe zukatan al’umma da kuma haifar da wani irin yanayi da zai tunkuda al’umma cikin rami, sabo da kuma kauce wa tafarki.

Na uku: Don sanar da al’umma ma’anar Imamanci (shugabanci) na shari’a a mahangar Musulunci da kuma abin da ya kunsa: Hakika irin hatsarin da ke tattare da rawar da bakar siyasar Umayyawa ta taka a bangare ma’anonin Musulunci abu ne da ya saba wa ka’idoji (na Musulunci), don kuwa rawar ta faro ne daga wajen manyan jami’ai wadanda suka rike manyan hanyoyin wayar da kan al’umma. Lalle wannan wani lamari ne da yake bukatuwa da bahasi da kuma dubi cikinsa.

Babu shakka Imam Husaini (a.s) yana sane da hakan, don haka ne ma ya fara kokarin shiryar da kuma wayar da kan al’umma dangane da hatsarin da suke fuskanta daga mulkin Umayyawa a matsayinsa na mulkin da ya saba wa dokokin da koyarwa irin ta Musulunci. Hakan kuwa ya biyo bayan tsarin da Mu’awiyya ya fito da shi ne na gado da kuma kama karya yayin da ya tilasta wa mutane suka yi mubaya’a wa dansa Yazid.

Ta haka ne Mu’awiyya ya sanya wani gagarumin dutse a kan tafarkin shugabanci na Musulunci, wanda mummunan tasirinsa ya ci gaba da yaduwa har zuwa wannan zamani namu da kuma yin hidima wa abokan gaban Musulunci nesa ba kusa ba.

Bisa la’akari da bukatocin Musulunci da kuma sharuddan da ya kafa kan shugaban, Imam Husaini (a.s) ya yi kokarin tabbatar da wannan lamari mai muhimmanci cikin zukatan al’umma ta hanyar jawaban da ya dinga yi a duk lokacin da ya sami irin wannan dama. Ga kadan daga cikin irin wadannan kalamai:

“Ya ku mutnne! Idan har kuka ji tsoron Allah kuma kuka san hakkokinSa, to hakan zai kasance mafi yarduwa gare ku, mu Ahlulbaitin Muhammadu (s.a.w.a) mu ne muka cancanta da rike wannan lamari (shugabanci) sama da wadannan da suke da’awar abin da ba su da shi, masu mulki da zalunci da danniya(5)”.

Da kuma fadinsa cewa:

“Bayan haka, hakika Allah Ya daukaka Muhammadu (s.a.w.a) a kan dukkan halittunSa, ya karrama shi da annabci sannan kuma ya zabe shi da manzanci, kana daga baya kuma Ya dauke shi zuwa gare Shi, lalle ya yi nasiha ga bayinSa (Allah) da kuma isar da sakon da aka aiko shi da shi. Mu kuma mune iyalansa, waliyansa, wasiyyansa, magadansa kuma wadanda suka fi cancanta ga wannan mukami nasa a kan sauran mutane. Sai dai mutane sun zaba wa kansu wannan mukami, amma dai mun yarda da haka, saboda tsoron rarrabuwa da kuma shaukin kiyaye zaman lafiyan al’umma, duk kuwa da cewa mun san mu muka fi cancanta da wannan al’amari sama da wadanda suka dare kansa. Don haka ga manzona gare ku da wannan wasika, ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa, a halin yanzu an kashe Sunna kana kuma an raya bidi’a, idan har kuka saurari zance na, to zan shiryar da ku zuwa ga tafarki madaidaici(6)”.

Ta hanyar wadannan kalmomi da ma wasunsu, Imam Husaini (a.s) ya sami damar bayyanar wa al’umma cewa Umayyawa dai ba su cancanci shugabancin al’ummar ba, saboda karen tsayen da suke yi ga tafarki da kuma koyarwa irin ta Musulunci. Haka nan kuma mutane sun fahimci tafarkin da ya wajaba duk wani shugaba musulmi ya bi, da kuma siffofin Musulunci da dole ne shugaba ya kasance yana da su, wadanda kuma a fili ana iya ganinsu a wajen Imam Husaini (a.s), saboda da kasantuwarsa renon annabci, dan sakon Musulunci kana kuma dalibin wahayi mai tsarki.

Wannan dai shi ne mahangar Musulunci dangane da shugabanci, wanda kuma shi ne babban dalili na wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) don yaye zanin zaluncin Umayyawa wadanda suka dare karagar mulkin musulmi.

Na Hudu: Uzurin dan’Adam ba zai kasance abin karbuwa ba a mahanga shari’a ta Musulunci matukar ya gaza wajen aikata aikin da ya hau kansa (wajibi). Don shi mutum a bisa shari’a ba halitta ce mai cin gashin kanta ba, face dai shi halitta ce da ke amsa bukatun sako na Musulunci, wajibi ne a kansa ya yi aiki da abubuwan da shari’ar ta tanadar masa, dole ne ya mika wuya da kuma sadaukarwa saboda ita. Hakika umurni da aikin alheri da kuma hani da mummuna da kuma jihadi don Allah da dai sauransu ba su kasance ba face hakikanin fassarar wannan ruhi da addinin Musulunci ya bai wa mabiyansa. Hakan kuwa ya yi daidai da ci gaban mutum a tafarkin koyi da sakon Ubangiji.

Don haka Imam Husaini (a.s) a matsayinsa na dan zakin Ali kuma jikan Annabi Muhammadu (s.a.w.a) kana kuma dan sakon Musulunci, ya kasance tsarkakakken shafi daga cikin shafukan sakon Musulunci, kuma rayayyen ma’ana ga dukkan bangarorinsa. Hakan dai shi ne ya sanya shi ya kasance mutum na farko da ya sadaukar da kansa ga sakon Musulunci a lokacinsa.

Babu makawa irin wannan sadaukarwa tasa ga sakon Musulunci ne ya sanya shi zaban tafarkin yunkuri da gwagwarmaya, don kuwa matukar in ba ta haka ba babu wani gyaran da za a iya yi. Muna iya ganin hakan ne kuwa ta hanyar jawabinsa kan dalilin kaddamar da wannan yunkuri nasa, inda ya ke cewa: “Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al’ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana Aliyu bn Abi Talib”.

Ta haka ne ya ke ganin zai iya saukar da nauyin da ya hau kansa a matsayinsa na mai tabbatar da shari’a a zamaninsa da kuma kare ta.

Wadannan dai su ne manyan abubuwan da suka sanya Imam Husaini (a.s) da sahabbansa suka kaddamar da wannan yunkuri mai nasara, wanda sautinsa ya mamaye ko ina, mai tabbatar da Musulunci, mai share fage ga ma’abuta juyi duk tsawon tarihi da kuma tabbatar da mutane kan tafarkin jihadi.


(1)- Al-Imam al-Husain na Abdullahi al-Alayili, shafi na 342 zuwa sama.
(2)- Daga baya dai Hur ya canza ra’ayi da kuma canza sheka, inda ya bar sansanin bata na Umayyawa zuwa cikin dakarun kare gaskiya karkashin jagoranci Imam Husaini (a.s) har ya yi shahada.
(3)- Dubi Muruj al-Zahab na al-Mas’udi.
(4)- Maktal al-Husain na Abdurrazzak al-Mukarram, shafi na 138.
(5)- Kadan daga cikin jawabin da ya yi wa mutanen Hur a Karbala.
(6)- Kadan daga cikin wasikar da ya aike wa mutanen garin Basra.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

As you found this post useful...

Follow us on social media!

About Author (504)

Administrator

Ina da Burin Isar da sakon Musulunci. amma kuma dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). . Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). Ina son haduwa da jama'a daban - daban,masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su). Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) a kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararren kuma sanannen mai ilimi kuma masa ni (Domin na samu damar bayyanawa duniya, Addini na, da ra'ayoyin Raunanan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba).

Leave a Reply
Translate

English French German SpainMore

Like Facebook

Share